Kannywood
Yanzu-yanzu: Allah yayi wa Darakta Aminu S Bono Rasuwa

Yanzu nan Majiyarmu ta samu wani babban rashi da masana’atar kannywood tayi wanda tayi rashin mai bada umurnin wato darakta aminu s bono rasuwa.
Sanarwa ta fito daga shugaban hukumar tace fina finai a jihar Kano Abba Elmustapha da ya wallafa a shafin na sada zumunta kamar haka.
Allah Yayiwa Shahararren Darakta a Masana’antarmu Kannywood AMINU S BONO Rasuwa.
Muna Addu’ar Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa Kurakuransa Yasa Aljanna Ce Makomarsa. Idan Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Kyau Da Imani.”