FEDERAL GOVERNMENT SABON TALLAFI GA MAGIDANTA MILLIYAN 15 A FADIN KASA.

FG N25000 CASH TRANSFER
Labaran Hausa

‘Yan maula sun fito: Jama’a sun yi wa jarumi Ali Nuhu ca kan taya Gawuna murnar nasara a kotu

‘Yan maula sun fito: Jama’a sun yi wa jarumi Ali Nuhu ca kan taya Gawuna murnar nasara a kotu

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Ali Nuhu, wanda aka fi sani da sarki ya yi martani bayan kotun daukaka kara ta tabbatar da Nasir Yusuf Gawuna a matsayin zababben gwamnan Kano na 2023.

A ranar Juma’a, 17 ga watan Nuwamba ne, kotun daukaka kara mai zama a Abuja ta tsige gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da soke nasarar zabensa na ranar 18 ga watan Maris.

Kamar yadda aka sani, masana’antar Kannywood na taka rawar gani sosai wajen tallata yan takara musamman a jihar Kano wacce take cibiyarsu. A kan samu rabuwar kai tsakanin yan fim inda kowa kan karkata zuwa wajen yan takara da yake muradi.

Majiyamu ta legit na ruwaito Kowa dai ya san Ali Nuhu Gawuna ya marawa baya a lokacin zaben gwamna amma suka sha kaye a wancan lokacin.

Don haka yanzu da kotun daukaka kara ta kai nasara bangaren dan takararsa, sai ya fito ya taya shi murna a shafinsa na.

Ga abinda jarumi Ali Nuhu ya rubuta a shafinsa.

“Ina taya ku murna kan nasararku a kotun daukaka kara @dr.nasirugawuna da @murtala_garo.”

Jama’a sun yi wa Ali Nuhu martani yi masa caa akan fustin ra’ayinsa.

Sai dai wannan sakon taya murna da jarumin ya aikawa su Gawuna bai yi wa mabiya shafinsa da dama dadi ba inda suka fito suka yi masa caaa a kai.

Majiyarmu ta Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin mabiyansa a kasa:

official_adam_bosz: “Toh yan maulla sun fara.”

_virus__official: “Kaima ka shiga cikin sahun kin Allah da kin qaddara.”

ashalaf90: “Abanza abanzazza ko gyezau Abba Zama daram dam da yaddar Allah.”

excellenc008: “Ban taɓa sanin jahili nake following ba sai yanzu. Oh forget! Ashe ba ɗan jihar ba ne shi ya sa zai so ƴan taɓare su karɓe ta don su tarwatsa ta. Toh Allah ya fi ku ya fi wanin ku mitsiyatan banza mitsiyatan wofi.”

c.e.o_albany_enterprises: “Wanda Yabi Bayan Zalunci Menene Hukuncinsa A Gurin Allah Director @realalinuhu.”

abseed__30: “@hafsieabdie taya zeyi yanzu munsan inda yadosa ai Daman can dan na nasune.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button