Labaran Hausa

‘Yan bindiga a jihar Zamfara sun kwashi mutane sama da guda 100 sabida sunki biyan kudin haraji

'Yan bindiga a jihar Zamfara sun kwashi mutane sama da guda 100 sabida sunki biyan kudin haraji

Najeriya – ‘Yan ta’addan da suka hana zaman lafiya a sassan jihar Zamfara dake Najeriya sun kwashi mutane sama da 100 a kauyukansu dake yankin Dansadau sakamakon bijirewa biyan harajin naira miliyan N110 da suka dora musu a matsayin kudin kariya.

Rahotanni daga jihar sun ce ‘yan bindigar da suka kwashi mutanen sun fito ne daga cikin magoya bayan fitaccen ‘dan ta’addan da ake kira Damina, wanda ya addabi mutanen wannan yanki na jihar Zamfara dake iyaka da jihar Kaduna.

Wani daga cikin mutanen yankin da ya tsallake rijiya da baya, yace tawagar ‘yan bindigar sun mamaye su ne bayan Sallar isha, inda suka musu kawanya, suka kuma tasa keyarsu zuwa cikin daji.

Daga cikin kauyukan da ‘yan bindigar suka kwashi mutanen da suka hada da mata da yara, akwai Yar Kasuwa da Unguwar Kawo da Kwanar Dutsi da kuma Sabon Garin Mahuta.

Majiyoyi sun ce Damina ya bai wa mutanen wadannan kauyuka ne mako guda ne domin biyan naira miliyan 110 da ya dora musu, ciki harda naira miliyan 50 da ya dorawa mutanen kauyen Mutunji saboda tseguntawa sojoji yadda suke motsawa a yankin da kuma naira miliyan 30 da ya dorawa mutanen kauyen Kwana da naira miliyan 20 da aka dorawa mutanen Sabon Garin Mahuta, sai kuma naira miliyan 10 na mutanen Unguwar Kawo.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da suka fi fuskantar ta’addancin ‘yan bindiga a Najeriya, wadanda suka mayar da kisa da kuma karbar kudin fansa suka zama ruwan dare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button