FEDERAL GOVERNMENT SABON TALLAFI GA MAGIDANTA MILLIYAN 15 A FADIN KASA.

FG N25000 CASH TRANSFER
Kannywood

Wanna Harkan Fim Na Kannywood Tayi Hannun Riga Da Allah – Mawaki Ibrahim Yala

Bayan kalaman abdallah amdaz sa yayi a hukumar hisbah bayan ta gayyace su inda anka nemi daya daga cikinsu su fadi tsakani da Allah shine ya fadi kalamai da sunka jawo cece kuce, shine mawaki kuma jarumi Ibrahim yala mawakin baba buhari “yau nijeriya riko sai mai gaskiya” ya nashi kalamai akan wannan maganar inda ya rubuta a shafinsa kamar haka.

Salamu Alaikum Wa Rahmatullah. Barkan Mu Da safiya Al’ummar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam Da fatan dacewa Duniya Da lahira Amin.

Wato Mafi yawan musibu suna faruwa ne daga kangarewa ɗaukar wa’azi Ko wasun Ku su janyo muku. NI Ibrahim Yala nasha yin maganganu Irin Na AMDAZ koma waɗanda suka fi nashi zafi Domin a samu gyara a wannan masana’anta Da Allah Ya kaddara Sai an ganmu Acikin ta.

Wallahi thunma tallahi wannan harkar tayi hannun riga Da Allah tuntuni Sai dai Idan bazamu fadi gaskiya Ba saboda son Rai Ko jahilci Na Rashin Sanin halal Da Haram. Wallahi Ni Bama ɗan dana haifa ba Ko Wanda Banda alaqa dashi indai sanadi Na Zai shiga fim bazan bari Ba.

Masana’antar da babu mai ganin girman Wani Saboda Yawancin mu mun zubar da mutuncin junan mu, babu albarka a abinda muke kira sana’a Saboda Mun kaucewa duk wani tsari na addini, babu mai sawa ko hanawa a Cikin masana’antar. Kunsan gaskiya Sai dai kubi son rai amma duk abinda aka faɗa ana aikatawa babu sharri ko son rai a ciki. wallahi ban taɓa tsintsr kaina a harkar da kullum take fita a raina ba Irin wannan harkar tamu. Na taɓa Magana da Wani akan yadda matan masana’antar da sukayi suna sukeyi na rashin kamun kai da gadara gurin sabawa tsarin addini, sai yace wadannan yaran Kusan su suke rike Da masana’antar domin ɗai ɗai Wanda Basu Baiwa kuɗi.

Shi Yasa zakaga yarinya tayi posting a bakin hotel Bayan kwashe kwanaki tana holewarta har ma kaga ta rubuta Alhamdu Lillah Sai kaga Kowa Na tura Mata WOW kinyi kyau Ko hoton alamar zuciya,ko wuta balbal. NI daku munsan sana’ar ta Ba fim bane sannan Haka wasu mazan Cikin Mu sun Zama abokan hulɗar Yan siyasa waɗanda basu Da juriyar Zama Babu kuɗi su miƙa ƙansu Ko su Zama kawalai ta kowacce Irin siga.

Idan nace Zan cigaba Da rubuta abubuwan dana Sani Game Da Wannan masana’antar gaskiya za’a sha mamaki Domin wasu abubuwan ma sun shafe Ni Kai tsaye wallahi. Allah Ka shiryar damu hanya madaidaiciya Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button