FEDERAL GOVERNMENT SABON TALLAFI GA MAGIDANTA MILLIYAN 15 A FADIN KASA.

FG N25000 CASH TRANSFER
Labaran Hausa

Nan da shekaru kadan ‘yan Najeria zasu daina fita Kasashen waje Karatu, cewar Prof Gwarzo

Nan da shekaru kadan ‘yan Najeria zasu daina fita Kasashen waje Karatu, cewar Prof Gwarzo

Fitattcen limamin wanzar da ilimi a Najeriya, kuma shugaban Jami’ar Maryam Abacha dake Kano da Maradi, Nijar, da jami’oin Franco-British dake Kaduna da Canadian International University dake Abuja, Farfesa Adamu Gwarzo, ya bayyana cewa nann ba da dadewa ba, ‘yan Najeriya za su daina tura ‘ya’yan su karatu jami’o’in waje.

Farfesa gwarzo ya bayyana haka a lokacin da yake duba aiki a Jami’ar Canadian dake Abuja a farkon wannan mako.

Majiyar leadership hausa ta ruwaito, Farfesa Gwarzo ya ce ya ga yadda ilimi ya bunkasa kasashe kamar su Faransa da Jamus da wasu manyan kasashen duniya, dalilin da ya sa ya ce a yadda aka maida hankali a Najeriya, nan ba da dadewa za a kai lokacin da jami’o’in mu sun ishe mu ba sai mun gita zuwa kasashen waje ba.

”Yanzu muna gina jami’o’i ne fitatatu da ke da komai da ake samu a jami’i’in kasashen waje, saboda haka babu dalilin da zai sa ka tura ‘ya’yan waje.

”Misali ka je jami’ar Maryam Abacha da ke Kano ka gani. Babu abinda za ka gani a jami’ar waje da babu a can. Mun yi haka ne domin muma namu a Najeriya su rika morar irin abinda ake samu a waje.

A karshe ya ce burin sa shine ya ilmantar da yara sama da Miliyan 1, ta sanadiyyar sa su samu ilimi kafin ya koma ga Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button