Kannywood

Na yafewa marigayi Aminu s bono duk kudi da nake binsa,cewar Murja Ibrahim Kunya

Na yafewa marigayi Aminu s bono duk kudi da nake binsa,cewar Murja Ibrahim Kunya

Shahararriyar mai amfani da kafar yanar gizo ta TikTok ‘yar asalin jihar Kano Murja Ibrahim Kunya ta bayyana cewar dukkan kudaden da take bin marigayi Darakta Aminu S Bono ta yafe masa.

Murja yayin da take mayar da martani a kan kiran da aka yi mata na cewar ta bayyana adadin kudaden da take bin marigayin.

Ta bayyana cewar har ga Allah ta yafe masa kudaden, kuma bata bukatar a biya ta.

Murja ta kara da cewar ita kanta idan da za ta ga wani wanda yake bin Aminu bashin kudi idan tana da su za ta biya masa ba tare da da wani bata lokaci ba.

Daga karshe ta yi masa addu’oin samun rahama inda ta ce tana yi masa fatan Allah ya karbi bakuncinsa ya kuma kyautata makwancinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button