FEDERAL GOVERNMENT SABON TALLAFI GA MAGIDANTA MILLIYAN 15 A FADIN KASA.

FG N25000 CASH TRANSFER
Kannywood

Na karɓi sammacin Kotu, amma har Mahdy ya baiyana a busa ƙaho bazan ƙaryata kaina ba – Amdaz

Jarumi kuma mawaƙi a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Abdallah Amdaz, ya ce ya karɓi sammacin kotu kuma zai bita da Hasbunallahu Wani’imal Wakeel, amma dai yace daga yanzu har Mahdy ya baiyana a busa ƙaho, bai ga kotu ko wani Ɗan Adam daya isa ya saka shi ƙaryata kansa ba.

Amdaz ya bayyana haka ne ranar Alhamis cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda yace ba awa 48 ba, har zaren agogo ya tsinke, babu wanda ya isa ya san shi bada haƙuri acikin haƙƙin Ubangiji, don haka duk abinda ya faɗa ya faɗa, bazai ƙaryata kansa ba akan wannan maganar.

“Tunda kun kasa kawo hujja ko ƙaryata abinda na faɗa, kawai ku karɓi gaskiya ku huta, kuyi Umarni da kyakykyawa kuyi hani da mummuna.”

Wani furodusa ne dai mai suna Mustapha Ahmad wanda aka fi sani da Alhaji Sheshe, ya maka Abdallah Amdaz a kotu kan kalamansa da ya yi a ofishin Hisbah ranar Litinin, wanda yake so kotu ta bawa Amdaz umarnin bada hakuri cikin awanni 48 bisa zargin bata masa suna.

NasaraRadio

AmanarTalaka

16/11/2023

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button