FEDERAL GOVERNMENT SABON TALLAFI GA MAGIDANTA MILLIYAN 15 A FADIN KASA.

FG N25000 CASH TRANSFER
Labaran Hausa

Matatar Man Kaduna Za Ta Fara Aiki A 2024 —Minista

Ministan Mai, Heineken Lokpobiri, ya ba da tabbacin za a kammala gyaran Matatar Mai ta Kaduna kuma ta fara aiki a shekarar 2024

Ministan Albarkatun Man Fetur (bangaren mai), Heineken Lokpobiri, ya bayyana cewa za a kammala gyaran Matatar Mai ta Kaduna (KRPC), kuma ta fara aiki a shekarar 2024 mai kamawa.

Ministan ya bayyana haka ne lokacin ziyarar da ya kai matatar ta Kaduna domin bane wa kansa yadda aikin gyaran ke tafiya.

Lokpobiri ya bayyana gamsuwarsa da yanayin tafiyar aikin, wanda ya ce ya yi nisa sosai, kuma yana da kwarin gwiwa za a kammala kuma matatar ta ci gaba da aiki kafin karshen shekarar 2024.

Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya za ta rika sanya ido tare da bibiyar duk masu ruwa da tsaki a gyaran Matatar Mai ta Kaduna, a kokarin gwamnatin na tabbatar da an kammala shi a kan lokaci.

Ministan ya bayyana cewa akwai bukatar gaggawar ta ganin matatar ta ci gaba da aiki domin bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma samuwar wadataccen makamashi a cikin gida — wadanda ginshikan ne na cigaban ƙasa.

Kafin jawabin ministan, Shugaban Rukunin Kamfanin NNPC, Mene Kari, ya ba shi tabbacin kammala gyaran da ake wa matatar kafin karshen 2024.

Mele Kyari ya ce, “Muna da ƙwarin gwiwar samun duk abin da muke bukata har a kammala aikin gyaran, wanda daga nan ’yan Najeriya za su fara ganin alfano.

“Muna son ganin bangaren tace lita 60,000 a kullum ya fara aiki ba tare da bata lokaci ba, mu fara samun kudade nan take, kafin mu fara wasu bangarorin ta yadda matatar za ta koma cikakken aiki.”

Ziyarar ta samu halarci kwamitin gyaran karatun mai na Najeriya da kuma shugabanni da manyan jami’an Rukunin Kamfanin NNPC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button