FEDERAL GOVERNMENT SABON TALLAFI GA MAGIDANTA MILLIYAN 15 A FADIN KASA.

FG N25000 CASH TRANSFER
Labaran Hausa

Malamin Makaranta Ya Shiga Hannu Kan Zargin Fyade

An kama wani malamin makarantar sakandare a Jihar Ogun bisa zargin yi wa wata budurwa fyade.

Olaniran da ake zargin, malamin lissafi ne a makarantar Ebenezer Grammar School da me Iberekodo, Abeokuta Jihar Ogun.

Kwamishinar harkokin mata ta jihar, Adijat Olaleye ce ta bayyana cewa an kama malamin ne a ranar Asabar, a lokacin da wata daga cikin mukarrabanta ta samu kira cewar wani malamin ya yi mata fyade.

Kwamishiniyar ta ce ma’aikatar ta je inda lamarin ya faru inda aka yi gwaje-gwaje tare da mika rahoton ga ’yan sanda.

“Daga baya mun tafi tare da ’yan sanda zuwa gidan wanda ake zargi, amma da aka kwankwasa ya ki bude kofar. Mun samu dan uwansa wanda shi ne ya taimaka mana muka shiga gidan,” in ji ta.

Adeleye ta bayyana cewa da suka shiga harabar gidan wanda ake zargin, “mun ji kukan yarinya tana neman agaji, kuma ’yan sanda sun taimaka mun kama Mista Olaniran Lateef Adewale, wani malamin lissafi na makarantar sakandare ta Ebenezer Grammar School Iberekodo, Abeokuta. ”

Kwamishinar ta kara da cewa yarinyar tana kuka a dakin malamin a lokacin da aka kama shi ta kuma zarge shi da yin lalata da ita da kuma yin barazanar kashe ta.

An tsare wanda ake zargin a hedikwatar ’yan sandan jihar Ogun domin ci gaba da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button