FEDERAL GOVERNMENT SABON TALLAFI GA MAGIDANTA MILLIYAN 15 A FADIN KASA.

FG N25000 CASH TRANSFER
Labaran Hausa

Majalisa Ta Yi Fatali Da Bukatar Tinubu Ta Kashe Biliyan 5 Wajen Sayen Jirgin Ruwa

A maimakon haka, majalisar ta ce za a yi amfani da kudin wajen ba dalibai bashi

Majalisar Wakilai a ranar Alhamis ta yi fatali da bukatar Shugaban Kasa Bola Tinubu ta kashe Naira biliyan 5 daga cikin kwarya-kwaryar kasafin kudin tiriliyan 2.17 wajen sayen jirgin ruwa.

A maimakon haka, majalisar ta bukaci a mayar da kudin wajen kara yawan kuɗin da aka ware domin ba dalibai rancen, wanda a baya aka ware wa biliyan 10.

Aminiya ta rawaito cewa matakin ’yan majalisar ba zai rasa nasaba da koke-koken da ’yan Najeriya suka rika yi ba tun bayan bullar labarin, inda suka ce ya zo a daidai lokacin da ’yan kasa ke korafin kuncin rayuwa.

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Abubakar Kabir (APC, Kano) ne ya bayyana hakan lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi jim kadan da kammala amincewa da kasafin a Abuja.

Ya ce daukar matakin ya zama wajibi la’akari da kudin da aka ware wa daliban a cikin kasafin ya yi kadan.

Abubakar ya kuma ce kwamitin ya kason da aka ware wa Ma’aikatar Tsaro daga Naira biliyan 476 zuwa 546 sakamakon ƙaruwar kalubalen tsaro.

Shugaban kwamitin ya kuma ce sun duba tare da amincewa da batun kara mafi ƙarancin albashin ma’aikata domin mika shi ga bangaren zartarwa.

Sai dai ya ce za su tabbatar suna sanya idanu ga bangaren zartarwa domin ganin sun yi abin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button