FEDERAL GOVERNMENT SABON TALLAFI GA MAGIDANTA MILLIYAN 15 A FADIN KASA.

FG N25000 CASH TRANSFER
Labaran Hausa

Magoya bayan Man United za su yi gagarumar zanga-zanga a Old Trafford ran Asabar

Ƙungiyar magoya bayan Manchester United mai ƙarfin iko mai suna 1958 ta yi kira ga magoya bayan United da su gudanar da zanga-zangar ta tsawon sa’o’ ɗaya kafin take wasan ƙungiyar da Luton Town a ranar Asabar.

Magoya bayan Manchester United sun fusata kan yadda iyalan Glazer, mamallakan ƙungiyar ke ci gaba da haifar da rashin nasara a kungiyar na shirin yin wani sabon salon zanga-zangar adawa da su Glazers din.

Daily Nigerian ta rawaito cewa, ana sa ran ƙarin zanga-zanga kafin wasan Premier na United a gida da Luton Town ranar Asabar yayin da magoya bayan ke sabunta kiraye-kirayen a kori Glazers.

Steve Crompton, mai magana da yawun 1958, ya ce kwanan nan an dakatar da zanga-zangar ne saboda mutuwar tsohon kyaftin din United, Sir Bobby Charlton, inda ya kara da cewa “amma za mu ci gaba da gwagwarmaya”.

“Mun gane cewa watanni 12 da suka gabata sun tabbatar da babu shakka cewa Glazers sun damu da samun kudaden kan su kawai ba nasara kungiyar ba.

“Ba su cancanci zama mamallakan Manchester, ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na duniya ba. Amma ba za su iya sayen soyayyar da muke yi wa ƙungiyar tamu ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button