Kannywood

Madalla Maikwashewa: Abdul Amart Maikwashewa ya sayawa iyalan Aminu s Bono gida

Madalla Maikwashewa: Abdul Amart Maikwashewa ya sayawa iyalan Aminu s Bono gida

A yau din nan Ƙungiyar Daraktoci ta PROFDA na gayyatar dukkan ƴan wannan masana’anta mai albarka ta Kannywood, zuwa taron addu’ar ɗan uwan su marigayi Aminu S. Bono.

Rana: Litinin 27-11-2023
Wuri: Social Welfare, Court road
Lokaci: 3:00 na yamma.

Allah ya bawa kowa ikon zuwa, a ranan zasu saka dukkan ƴan uwan su da suka riga mu gidan gaskiya acikin Addu’a kamar yadda sunka fitar da sanarwa jiya.

A wajen ne anka samu labari mai dadi babban mai shiryawa furodusa yayiwa iyalan margayi mai bada umurni darakta Aminu s bono goma ta arziki kamar yadda daya daga cikin yan masana’atar Kannywaood na fitar da labarin a shafinsa na sada zumunta Al-amin chiroma.

Babban Furodusa, Abdul AMART, Wanda aka Fi sai da Mai Kwashewa, ya saya wa iyalan Marigayi Director Amuni S. Bono Gidan zama.

Masana’antar Kannywood na ci gaba da yi wa Abdul Amart godiya marar adadi, gami da addu’ar Allah Ta’ala Ya saka masa da mafificin alheri, ameeen.

A daidai lokacin da ake ci gaba karanta addu’o’in fida’i ga ruhin Malam Aminu Suraj Bono. Allah Ya rahamshe shi, ameeeeen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button