Labaran Hausa

Kotu zata yanke hukunci kan shari’ar zaben Gwamnan jihar Nasarawa a gobe

Kotu zata yanke hukunci kan shari’ar zaben Gwamnan jihar Nasarawa a gobe

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta sanya ranar Alhamis domin yanke hukunci kan shari’ar zaben gwamnan jihar Nasarawa.

Gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC ne ya shigar da kara kan hukuncin kotun tirabunel da ta ce ba shi ya lashe zaben ba inda ta bayyana David Ombugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben Nijeriya INEC ta bayyana Sule a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar ta Nasarawa da aka gudanar a ranar 18 ga Maris din shekarar nan, sai dai Ombugadu ya garzaya kotu inda ya kalubalanci nasarar ta Sule.

A cewar INEC, Sule ya samu kuri’u 347,209 inda ya doke abokin hamayyarsa wanda ya samu kuri’u 283,016.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button