FEDERAL GOVERNMENT SABON TALLAFI GA MAGIDANTA MILLIYAN 15 A FADIN KASA.

FG N25000 CASH TRANSFER
Kannywood

Kannywood sunfi hisbah amfani ga al’umma da gyaran tarbiyya – cewar Saddam Ibrahim

Wani fitaccen mai amfani da kafar sada zumunta ta Facebook saddam Ibrahim ya wallafa a shafinsa cewa Kannywood din nan da ake gani tafi hisbah har da gwamnati ga al’umma.

Saddam ya wallafa rubutun ne a shafinsa na sada zumunta jim kadan bayan zaman hisbah da kannywood inda yake nuna da cewa ita fah kannywood din nan amfaninta yafi na hisba kai harda gwamnati.

Kannywood sun fi Hisbah amfani ga al’umma da gwamnati. Sun fi Hisbah generating revenue da samarwa matasa aikin yi. Idan ma tarbiyyar ce sun fi Hisbah iya amfani da hikima wajen gyara tarbiyya. Domin ban taba ganin inda mutumin banza ya yi nasara a movie din su ba. It is highly predictable. Movie din su kullum black and white ne.

Sannan yan siyasa su kiyayi batawa Kannywood rai akan Hisbah saboda yan Kannywood influencers ne suna yin amfani lokacin zabe. Idan ku ka cire dan munafuncinan na mutane na yanzu don ace suna goyon bayan yaqi da badala ba wani taimako da Hisbah za ta iya muku lokacin zabe.

Girmama masana’artar Kannywood da tallafa mata don ta samu bunkasa abu ne mai muhimmanci ga jihar Kano.”

Hausaloaded ta samu tattara martanin mutane a karkashin wannan rubutu.

@Abubakar Isah hassan cewa yake :

Hahhhhhhh. Anya Saddam Ibrahim kana so a zauna lafiya? Kai ko ɗan munafurcin nan irin na mutanen Arewa baka yi ka ɗan sassauta kar masu ƙwaƙwalwar dusa su taso ka gaba. Anya ba kai bane Aljanin da ake muhawara game da existence ɗinsa ba.

@abdul Mohammed cewa yake :

Gaskiya ne, ita hisbah ba musulunci take wa aiki ba, yaki take da zamani. A tarihin duniya babu wata al’umma data yi nasarar kawar da badala ko rage ta da wannan tsari. Babu yadda tarbiya zai wanzu a yanayin tsananin jahilci da fatara.

@shehul islami aminu bello ga abinda yake cewa:

Wannan jumlar ta bada citta wallahi ” Idan kuka cire ɗan Munafuccin nan na mutane”.

@Dahiru Muhammad hashim cewa yake :

Malam sadam bai fito ba sai da ya shirya fa mai abin faɗa baya faɗa.

@anexco anas Ag fulatan cewa yake :

Sai yau nakara kallon hotonka sosai nagan Kuna kama da Musa mai Sana’ana sosai

Amma fa tawani gefen magananka akwai kamshin gaskiya.

@ouummey Abdullahi aminu cewa yake :

Ikon Allah, wane amfani kannywood keyi wa al’umma, can You pls give an example of one?.

@saddam ibrahim ga amsar da yake bayarwa :

Ouummey Abdullahi Aminu Samar da aikin yi. Kin san adadin matasan da ke cin abinci ta wannan harkar kuwa? Daga camera men zuwa marubuta zuwa masu sharar office zuwa jarumai da kama hayar offices. Ga tax da dukkan wani kamfanin production ke bawa gwamnati. Da wannan ake hadawa gwamnati ta samu kudin yin ayyuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button