Kannywood

Irin mutuwar Darakta Aminu S Bono tana bukatar a binciki gawarsa domin gano sababin mutuwarsa

Irin mutuwar Darakta Aminu S Bono tana bukatar a binciki gawarsa domin gano sababin mutuwarsa

Mutuwar fitaccen jarumi mai bada umurni a hausa fim aminu s bono ya sanya wasu yan arewa cewa yakamata a yi bincike mutuwar jarumin ta fuju’a da yayi saboda a wasu dalillai da sunka kawo.

Zamu fara da ra’ayin Aliyu dahiru aliyu wanda fitaccen ma’aboci da kafar sada zumunta ta facebook inda ya bayyana ra’ayinsa kamar haka.

“Irin mutuwar Aminu S. Bono tana bukatar a yi mata autopsy a gano me ya kasheshi. Haka kawai ana zaune kalau da mutum a ce cikinsa ya murda kuma wai ya mutu ya saba da al’ada, musamman ga mutumin da aka san ya shiga rigimar addini ko ta siyasa.

Binciken me ya kashe mamaci yana hana a yi masa addu’a ne? Shirme ne a ce ana bukatar a binciki me ya kashe mutum kai kuma ka ce “kawai addu’a za a yi masa.” Ba za a iya hada biyun ba ne?

Masu cewa kuma binciken me ya kashe mutum (autopsy) rashin tauhidi ne jahilai ne na gaske. Don ba ka ganin abin da ya kashe mutum sai ka ce binciken abin da ya kasheshin rashin tauhidi ne?

Yanzu da yanka wani aka yi ka ga jini za ka ce kawai a wuce gurin Allah ne ya kasheshi ne? Ko ba a iya kashe mutum da abin da ba a gani ne? Meye laifin bincike kawai don a magance matsala idan da an sameta don gaba?.

Daga cikin abin da nake rokon Allah akan mutuwa akwai fatan na mutu da daddare a asibiti mai kyau. Don wasu dogon suma suke da safe a binnesu bayan awa biyu. To sai ka ga a marasa lafiyar turawa wasu sun shekara a dogon suma (coma) kuma sun farfado sun ci gaba da rayuwa. Amma mu a nan ka taba ganin wanda aka ce ya yi 24-hours a sume ba a binneshi ba? Sai dai idan a asibiti ne, su ma wasu idan ba a cika musu kudinsu sun saki mutum an binneshi da ransa ba.

Cewa aka yi idan mutum ya mutu to a gaggauta yi masa jana’iza. Ba wai cewa aka yi ku yi gaggawar binne mutumin da ba ku tabbatar ya mutu ba. Ku dinga kai gawarwaki asibiti domin tabbatar da mutuwarsu.”

Ita ma hajiya Rahma abdulmajid tana daga cikin masu amfani da kafar sada zumunta inda itama ta bayyana ra’ayin ta da cewa yana da kyau ayi bincike irin wannan mutuwar duba da irin hujjojin da ta kawo.

“MUTUWAR AMINU BONO…

Wannan ita ce mutuwar Fuj’ah ta biyu da wani Director yayi a Kannywood. Shin lokaci bai yi ba ke nan da za a rika rungumar binciken zamani irin Autopsy don gane musababban irin wannan farat daya?
A fahimta fa, binciken musababbin mutuwa ba ja da kaddara ba ne, kawai sanin musababbi ne, wanda zai iya zama sanadiyyar ceton wasu ko gano masu hannu a wani laifin.

ALLAH YA JIKAN MALAM AMINU”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button