Irin Mutuwar Aminu S Bono Tana Bukatar A Binciki Gawarsa Domin Gano Sababin Mutuwarsa, Cewar Aliyu Dahiru Aliyu

Irin mutuwar Aminu S. Bono tana bukatar a yi mata autopsy a gano me ya kasheshi. Haka kawai ana zaune kalau da mutum a ce cikinsa ya murda kuma wai ya mutu ya saba da al’ada, musamman ga mutumin da aka san ya shiga rigimar addini ko ta siyasa.
Binciken me ya kashe mamaci yana hana a yi masa addu’a ne? Shirme ne a ce ana bukatar a binciki me ya kashe mutum kai kuma ka ce “kawai addu’a za a yi masa.” Ba za a iya hada biyun ba ne?
Masu cewa kuma binciken me ya kashe mutum (autopsy) rashin tauhidi ne jahilai ne na gaske. Don ba ka ganin abin da ya kashe mutum sai ka ce binciken abin da ya kasheshin rashin tauhidi ne?
Yanzu da yanka wani aka yi ka ga jini za ka ce kawai a wuce gurin Allah ne ya kasheshi ne? Ko ba a iya kashe mutum da abin da ba a gani ne? Meye laifin bincike kawai don a magance matsala idan da an sameta don gaba?