FEDERAL GOVERNMENT SABON TALLAFI GA MAGIDANTA MILLIYAN 15 A FADIN KASA.

FG N25000 CASH TRANSFER
Labaran Hausa

Ina Addu’ar Kada Allah Ya Ba Ni Abin Da Mutane Ba Za Su Amfana Ba — Alhaji Aminu Dantata

Muna yara muna sayen kwai guda 12 kwabo daya.

Abu daya da za ka iya bayyana Alhaji Aminu Dantata shi ne dogo a siffa da kuma shekaru da kuma tsawon shekarun da ya dauka yana tara dukiya da kuma ilimin rayuwa.

Ya dauki tsawon shekara 70 yana gudanar da kasuwancin da ya shafi fatauci da gine-gine da harkar banki da abin da ya shafi muhalli da man fetur da iskar gas.

A wannan tattaunawa ya yi bayani kan gwagwarmayar rayuwarsa kamar haka:

Kasancewarka mutumin da na fara sani wanda ya ce ya yi karatu a makarantar da mahaifinsa ya gina, yaya abin ya kasance a wancan lokaci?

Mahaifinmu ne dai ya kafa wannan makaranta ce bisa abin da ya koya a kasashen waje. An haifi mahaifinmu a Nijeriya a garin Bebeji, bai yi ilimin boko ba.

Lokacin da Turawa suka zo sun so su danne ilimin addinin Musulunci. Sai dai shi da ’yan uwansa sun samu ilimin addini ga kuma harkar kasuwanci.

Shin Alhassan Dantata ya fara kasuwanci a Nijeriya ne kafin ya tafi Ghana?

Mahaifiyarsa ’yar kasuwa ce domin ta fito daga zuriyar da ake kasuwanci a wani yanki na Njiar lokacin muna hade kafin Turawa su raba mu.

To wane irin kasuwanci ya yi a Ghana kuma tsawon wane lokaci ya dauka a can?

Ina ganin bayan mahaifinsa ya rasu sai mahaifiyarsa ta tafi da shi Ghana, saboda tana da malamai a can. Ya fada mana cewa ya dade a can kafin ya dawo Nijeriya saboda a can ya yi aure.

A lokacin ta ruwa suke bi saboda ba hanyar jirgi ballanatana ta mota.

Shin zaman da ya yi a Ghana da malamai shi ya sa ya bude makaranta ga ’ya’yansa?

A’a, ita wannan makaranta ba wai ta ’ya’yansa ba ce kawai. Makarantar da muka yi a wancan lokaci makaranta ce ta allo, wacce ta kunshi mu ’ya’yansa da ’ya’yan ma’aikatansa da kuma makwabta.

Ba ka dade a makarantar ba sai ka kama harkar kasuwanci kai-tsaye?

Dukkan ’yan uwanmu sun yi karatun addini da na boko a wannan makaranta. Za su je da kafa su dawo gida. Har yanzu makarantar tana nan.

Wane lokaci ka fara kasuwanci, bayan kammala karatun firamare?

A lokacin hutu mahaifinmu yana koya mana yadda ake kasuwanci. Kasancewar a wancan lokaci babu motoci duk kayayyakin da mahaifinmu ke sayarwa ana kawo masa ne a rakuma da jakuna.

To da jakin kuke amfani wajen sayar da kayan?

Eh, za ka yi mamaki idan ka ji cewa a wancan lokacin ’yan motocin da ke aiki sukan dauki kwana hudu zuwa biyar kafin su je wurin da za su.

Haka akwai wuraren da idan motar ta kai ku to sai dai ku kwashi kayan a jaki ku karasa.

Saboda haka muka saba yawonmu a jakuna da rakuma, daga baya kuma muka samu kekuna.

Akwai lokacin da ka zama wakilin mahaifinku don kula da kasuwanci a Sakkwato ko?

Kwarai, sai dai kafin wannan lokaci na fara karbar aiki a wurin yayana Ahmadu Dantata a garin Bichi a 1947.

A wancan lokacin kana matashi?

Eh, ina dan shekara 17 saboda a zuriyarmu yara na fara kasuwanci tun suna da kananan shekaru, kamar bakwai, takwas.

Mahaifinmu yana fada mana cewa idan mutanen da suka kawo masa kayayyaki irin su gyada a kan rakuma da jakuna da shanu yakan ce mana mu dauki kwarya mu zuba ruwa da gishiri mu rika bai wa dabbobin suna sha sai ake biyanmu anini-anini da kuma kwabo-kwabo.

Bayan mahaifinku ya rasu kasuwanicn gidan naku ya tsaya ko kuma ’yan uwanka sun ci gaba da aiwatarwa?

Kafin mahifinmu ya rasu ya kafa kamfani mai suna Alhassan Dantata and Sons.

Ya kira yayanmu Alhaji Ahmadu da Alhaji Sanusi ya fada musu cewa rashin lafiyar da yake yi ba na tashi ba ne.

Lokacin bai fi shekara 70 ba. Ya fada musu cewa yana so su ci gaba da gudanar da kamfaninsa.

Kafin su ce komai sai ya ce musu na san wasu ba za su yarda da abin da na yanke ba.

Ya ce Alhaji Ahmadu ya zama Manajan Darakta.

Bayan ya rasu yaya aka yi?

Bayan ya rasu sai suka tara mu suka ce Baba ya ce mu ci gaba da gudanar da kamfanin nan, amma mene ne ra’ayinku?

To sai su suka ce suna so su yi kasuwanicnsu daban. Shi babban ya grime ni da shekara biyar yayin da dayan kuma ya girme ni da shekara daya da rabi.

Sai suka ce za su dauki dukiyarmu su kai wa hukuma idan mun kai shekara 18 sai a ba mu. To hakan kuwa aka yi.

To ba a raba gado ba ke nan sai kowa ya dibi rabonsa?

A’a an raba gado. Shi babban ya dauki nasa ragowar namu aka kai wa hukuma.

Wannan shi ya kawo aka samu kamfanoni biyu ke nan, Alhassan Dantata and Sons da Sanusi Dantata and Sons shin sun yi gasa da juna?

Babu wani batun gasa da juna a tsakanin kamfanonin biyu. Mun ci gaba da ayyukanmu har zuwa rasuwar Alhaji Ahmadu Dantata inda suka janyo Alhaji Garba Maisikeli ya zama yana da fadi-a-ji a kamfanin.

A lokacin kai ne Manajan Darakta ko?

A’a shi Alhaji Garba Maisikeli ne Manajan Darakta ni kuma Mataimakinsa.

To daga bisani ka fita daga kamfanin, haka ne?

A’a ban fita ba. Ana nan ana tafiya sai wasu daga cikin ’ya’yan Alhaji Ahmadu Dantata suka nemi sanin abin da yake faruwa a kamfanin, to sai muka yanke shawarar cewa a bude musu asusun banki don kayayyakinsu da kuma yadda za su rika karbar bashi ko riba da sauransu.

Shin wannan ne ya janyo ka fara bude naka kasuwancin?

Tun daga lokacin da muke tasowa ina kokarin kwaikwayon mahaifinmu wajen sayen filaye.

Yana fada mana yadda abubuwa suke, cewa kasuwancin filaye abu ne mai kyau.

Ko wannan wuri da muke mahaifinmu ne ya saye shi. Mahaifinmu ya san darajar fili ya kuma mallake shi a ko’ina a kasar nan musamman a kusa da tasoshin jiragen kasa.

Saboda muna ajiye gyada kafin a dauke ta zuwa kasashen waje.

Kuma a wancan lokaci abin na da araha, domin wuraren da ake maganar miliyoyin Naira ko biliyan a yanzu a da bai fi fam 500 ba.

Za mu iya cewa asalin dukiyarka daga harkar filaye ka samu?

Eh, ba wai ni kadai ba, da yawa daga cikin zuriyarmu suna yin wannan kasuwanci saboda mun gada daga mahaifinmu.

Za ka iya fada mana yawan filayen da kake da su kuma a wadanne wurare?

Ba na jin zan iya fada maka yawan filaye ko gidajen da nake da su a yanzu a duniya ba wai a Nijeriya ba.

A Nijeriya kaf babu inda ba ni da fili. A duk inda na san ba ni da wata dama to ina mallakar fili a wurin, ina da shi a kasar Saudiyya da Dubai da Alkahira a Masar da Ingila da Jamus da Amurka.

Na san cewa kana da jirgin sama naka na kanka, kana yin amfani da shi wajen ziyartar wandancan kasashe da kake da filaye ko gida a wurin?

Dalilin da ya sa na fara sayen jirgi domin in rika amfani da shi ne don zuwa wuraren da babu manyan jirage da suke sauka a wurin ko kuma babu kyawun hanya.

Na fara sayen jirgi a 1966. Kafin a kashe Sardauna. Akwai wani lokaci wasu mutane daga Nijar suka zo wajen Sardauna suka fada masa cewa suna da wata masana’anta a wani gari mai suna Malbaza amma ba su iya sayar da simintin da suke yi.

Sai Sardauna ya kira ni ya ce in je ko zan iya taimaka musu. Muka je Nijar a mota lokacin ban sayi jirgi ba. A nan dai muka saye dukkan simintin nasu.

Amma sai ya zama mutanen garin sun damu da abin matuka suna ganin yaya za a yi wani ya zo daga Nijeriya ya saye musu kaya.

Sai na dawo na fada wa Sardauna abin da ya faru.

Amma Sardauna ya taimake ka ya ba ka kwangiloli masu yawa yadda ka zama na kusa da shi, haka ne?

Gasiya ne, amma ba ni kadai yake yi wa hakan ba, idan ya san za ka iya abu ko kai dan kasuwa ne ko dan siyasa ko dan boko zai iya cewa ka zo ka yi abu.

Na yi zaton kana daga cikin mutanen da kuka taimaka wa wasu jam’iyyun siyasa a yankin Arewa?

Ba wai taimaka wa ’yan siyasa na yi ba, ni ma ina daga cikin ’yan siyasar.

Sardauna ya kafa Kamfanin Bunkasa Masana’antu na Arewa (NNDC), shi wannan kamfani an kafa shi ne don ya tallafa wa harkokin kasuwanci na gwamnati tare da daukar nauyin kasuwancin daidaikun mutane, kuma ka san wani abu wallahi ba su tambayarmu mu ba su wani abu kafin su taimaka mana koda kuwa ta wajen bayar da kwangila ko karbar bashi.

Kai akwai lokacin da Sardauna ya nemi kamfanonin da suke aiki a Nijeriya su rage karfinsu su bar ’yan Nijeriya su karba daga gare su, kamfanoni kamar su UAC da FCO da GBO.

Mutane da dama daga shekarun 1970 ba su san cewa ka taba siyasa ba har ka taba zama mamba a Majalisar Wakilai ba?

Lokacin da Turawan Birtaniya suka so su bai wa kasar nan ’yancin kanta sun so ’yan Arewa su shiga cikin abin saboda sun san cewa muna da gaskiya da amana.

Lokacin da aka fara siyasa ina Jam’iyyar NEPU, na hadu da Malam Aminu Kano lokacin yana Bauchi.

Lokacin ana kiran Jam’iyyar NEPA. Yayin da Malam Aminu ya shiga NEPA sai suka yi kokari canza ta zuwa NEPU.

A wancan lokaci sun so in zama shugaban matasa saboda a lokacin ina da babur ina yawo ina karbar kudi daga ’yan kasuwa muna kai wa jam’iyya.

A wancan lokaci ina tunawa yayana Alhaji Ahmadu yana Jam’iyyar NPC.

Haka ina tuna yadda mahaifina yake tare da masarauta. Yana zuwa wurinsu sannan sarakai suna zuwa wurinsa.

Ni kaina ina iya tuna lokacin da na kwana a gidan Sarki saboda uwargidansa (Sarki Abdullahi Bayero) kawar mahaifiyata ce.

Za a iya cewa hakan shi ya sa ka janye daga NEPU?

Zan iya cewa eh, domin na san mahaifina ba zai ji dadi ba ya ga dansa yana yakar masarauta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button