Labaran Hausa

Hukumar kididdiga ta Najeriya ta fitar da ma’aunin tantance tashin farashin kayayyaki

Hukumar kididdiga ta Najeriya ta fitar da ma’aunin tantance tashin farashin kayayyaki

Yayin da ma’aunin tashin farashin kayan masarufi ya kai kashi 27.33% bisa rahoton hukumar kididdiga ta Najeriya, masana sun ba da shawarar komawa kan kananan sana’o’i don samun mafita.

Akasarin kayan da Najeriya ke bukata a kan shigo da su ne daga kasashen waje domin ‘yan masana’antun Najeriya da ke samar da ayyukan yi sun dade da durkushewa.

Hakika da yawa daga talakawa ba sa fahimtar alkaluman kididdiga sai lokacin da su ka shiga kasuwa su ka ji dahir na yadda farashin kaya ke ninkawa, kuma hatta kayan da ake samarwa a cikin gida ba su tsira ba don tsadar sufuri da ya ta’azzara sakamakon tashin farashin man fetur da ake shigo da shi daga ketare.

Masanin kmiyyar kididdiga Farfesa Sadik Umar Abubakar Gombe, ya ce tun da ba wani shirin raya masa’antu, to yana da muhimmanci duk iyalai su farfado da sana’o’insu na kaka-da-kakanni.

A wani shirin raya sana’a, daraktan sana’o’in hannu na hukumar ba da shaidar sana’a ta Najeriya NBTE Muhammad Abbati ya ce su na da manhajar auna kwarewar masu sana’a don samar da dogaro da kai.

Gwamnatin Najeriya ta bakin Ministan yada labarai Muhammad Idris, ta ce ta na sane da kuncin rayuwa biyo bayan cire tallafin man fetur amma ta na daukar matakan rage radadi da ya dace jihohi ma su bi sahu.

A Najeriyar yanzu haka gidajen da kan dora tukunya sau uku a wuni tsakanin talakawa da su ka fi rinjaye na zama zakka, da hakan ya sa wajibi ne kowa ya sauya dabara zuwa wani zabi da bai sabawa doka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button