HUKUMAR HISBAH DA ‘YAN KANNYWOOD.

SAI KAGA YARINYA TAZO KANO TANATA YIN ABINDA BAI KAMATA BA AMMA DA AN KAMA TA SAI KAJI TACE ITA YAR FILM CE !
KO MAI HAKAN YAKE NUFI ?
Hakan ne yasa Shugaban Hukumar tace Fina-finai ta jahar Kano Alh. Abba El-mustapha yace da sake kuma lallai ne kowa yazo ayi masa REGISTA dan acire Bara gurbi daga cikin su duk da dai wasu marasa kishin Kano da masana’antar ta kannywood nata kokarin ganin sun dakile aniyar tashi ta kawo gyaran a wani salo na yin korafin wai su buza su iyaba, wasu ma na cewa wai basu da halin biyan kudin rigistar. Kudin da baitaka Kara ya karya ba.
To yanzu Alhmdulillah gaskiya tayi halinta gashi manufar Alh. Abba El-mustapha ta fito fili domin a kaman da hukumar Hisbah suka gudanar karkashin jagorancin Mlm Aminu Daurawa ya nuna cewa da yawa daga cikin matan da aka kama suna aikata abinda bai kamata ba na ikirarin su yan masana’antar ta kannywood ne.
Saide abin takaici harkawo ya wannan lokaci su wadanda suke kalubalantar ayi regista ga yan masana’antar ta kannywood sun ja baki su sun yi shiru, sun kuma kasa zuwa su karbo su tunda sun yarda kowa ma dan masana’antar ta kannywood ne, Kuma Suna yarda masana’antar ta cigaba da zama ci barkatai yayin da wasun Suma suke cewa ai ita masana’antar kannywood tamkar kasuwa ce kowa ma in yazo da hajarshi kawai ya siyar babu bukatar ace lallai sai anyi musu regista.
Muna fata a yanzu dai alumar jahar Kano tare da masu kishin masana’antar ta kannywood sun fahimci dalilin Alh. Abba El-mustapha na Kara kawo tsarin lallai kowa sai yazo yayi regista domin a cire bara gurbi daga cikin yan masana’antar tare da kawowa jahar Kano cigaba mai dorewa.
Musu iya magana de na cewa:
DA DAN GARI AKE CIN GARI ASABO DA HAKA INA DA YAKININ DUK ABIN EL-MUSTAPHA YACE A GYARA TO YASAN KUSKURE NE.
Signed:
Abdullahi Sani Sulaiman
Jami’an Hulda da jama’a na
Hukumar tace Fina-finai ta jahar Kano.
SAI GODIYA