FEDERAL GOVERNMENT SABON TALLAFI GA MAGIDANTA MILLIYAN 15 A FADIN KASA.

FG N25000 CASH TRANSFER
Kannywood

Hadiza Gabon ta kai wani mutum ƙara a Kotu bisa zargin ɓata mata suna

Jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu (Gabon), ta maka wani mutum mai suna Bala Musa, a gaban wata kotun Majistare da ke zamanta a Titin Daura, a jihar Kaduna bisa zargin ɓata mata suna.

Lauyan Hadiza Gabon, Barista Mubarak Sani, ya ce wacce yake karewa ta fuskanci munanan kalamai da kuma cin mutuncin daga jama’a saboda sharrin da wanda ake kara ya yi mata.

Bugu da ƙari yace, mutane musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo sun kira Gabon da macuciya, wacce ta riƙa cin kuɗaɗen Musa ta kuma ƙi auren sa, zargin da aka tabbatar da cewa karya ne.

Sai dai kuma wanda ake tuhumar, ta bakin lauyansa, Naira Murtala, ya musanta zargin, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.

Alkalin kotun, Shamsudeen Sulaiman, ya bayar da belin wanda ake kara da sharadin ya gabatar da wasu amintattun mutane biyu mazauna jihar Kaduna kuma dole ne su kasance ma’aikatan gwamnati, sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba domin mai ƙara ya gabatar da shaidu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button