Labaran Hausa

Gwamnatin jihar kano ta tura karin dalibai guda hamsin 50 karatu zuwa kasar India

Gwamnatin jihar kano ta tura karin dalibai guda hamsin 50 karatu zuwa kasar India

Kashi na biyar na dalibai 50 daga cikin dalibai 1,100 da suka kammala karatun digiri na farko da gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin karatunsu a kasashen waje, sun tashi zuwa kasar Indiya domin yin karatun digiri na biyu a fannoni daban-daban.

Wadanda suka ci gajiyar shirin sun tashi daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano zuwa Legas a cikin jirgin Max Air da misalin karfe 7:30 na safiyar ranar Juma’a, inda kwamishinan ilimi mai zurfi Dakta Yusuf Kofarmata da sauran jami’an gwamnati suka halarcin bikin tashin na su.

Daga Legas kuma za a kai su Indiya cikin jirgin Air Peace da karfe 2:00 na rana.

Daily Nigerian Hausa na ruwaito,da yake jawabi bayan tashin jirgin, Dakta Kofarmata ya ce tafiyar rukunin na biyar na daliban ci gaba ne da cika alkawarin da gwamnatin jihar kano ta dauka tura ɗalibai sama da dubu daya zuwa kasashen waje domin yo karatun digiri na biyu kyauta a shekarar 2023/2024.

Ya ce wadanda suka ci gajiyar tallafin, idan sun isa kasar Indiya, za a kai su jami’o’i daban-daban da suka hada da Sharda, Symbiosis, Mewar, Sri Sai, Swarnnim da Kalinga domin fara karatunsu na Digiri na biyu a fannoni daban-daban.

Dokta Kofarmata ya bayyana cewa daliban sun kammala karatun digiri na farko ne wadanda aka zabo su bisa la’akari da kwazon da suka yi a matakin farko.

Kwamishinan ya yi bayanin cewa wadanda suka ci gajiyar shirin za su yi karatu ne a fannonin daban-daban da ake bukata a duniya domin cike gibin ma’aikata a jihar da ma kasa baki daya.

Kwamishinan ya bayyana cewa, bayanan da gwamnatin jihar ta samu na cewa wadanda suka ci gajiyar shirin sun riga sun fara karatunsu kuma suna ci gaba a fannoni daban-daban.

Ya kuma bayyana cewa kimanin mutane 30 daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, bisa la’akari da yadda suke gudanar da karatunsu, tuni cibiyoyin da suke karatu suka dauki nauyin karatunsu a matsayin ma’aikatan wucin gadi kafin kammala karatunsu.

Ya ce wadanda suka ci gajiyar shirin sun kuma yaba wa gwamna Yusuf bisa irin karamcinsa da kuma cika alkawuran yakin neman zabensa na farfado da manufofin da tsohon gwamna, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bullo da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button