Labaran Hausa

Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya dauki nauyin jinyar Abdurraba wanda allurar cancer ta canza masa halitta

Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya dauki nauyin jinyar Abdurraba wanda allurar cancer ta canza masa halitta

Bayan fitar sanarwa dalibi Abdurraba ya yake fama da ciwon cancer da ta canza halittarsa wanda akwai ban tausai sosai, wanda majiyarmu ta samu daga maibada shawara ta musamman akan tallafi da agaji fauziyya d suleiman ta wallafa wannan sako na tallafi daga mai girma gwamna jihar Kano abba kabir yusuf (abba gida gida).

“Alhamdulillah, bayan sakonni da mutane ke ta turo mana daga ko’ina game da wannan bawan Allah ni da Baba Ali SSA HealthAffairs, mun sanar da mai girma Gwabnan Kano HE. Abba Kabir Yusuf halin da wannan bawan Allah ke ciki.

A kuma yau din Bava Ali ya tashi tashi takans ya je har garin su Abdurraba ya ga halin da su ke ciki, sannan ya sanar da su kulawarsa game da lafiyarsa gabadaya mai girma Gwabna ya dauki nauyi, duk da cewar aikin da zaa yi masa ba yanzu ba ne, asibitin Malam Aminu Kano yanzu sun dora shi akan shan magunguna na tsahon lokaci kafin ciwon ya dan sace sanna ayi aikin, Baba Ali ya tabbatar musu da duk abun da ya tashi koma menene da asibitin suka bukata su kira kaitsaye zaa yi musu, bisa umarnin mai Girma Gwabna.”

Abdurraba dalibi wanda har yayi bautar ƙasa wanda kafin wannan ciwon ya same shi Masha Allah, amma yanzu duba kaga yadda hallitarsa ta canza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button