Kannywood

Duk ‘yan kannywood ‘yan iska ne fasikai ne zindikai shedanu masu yada fasadi a bayan kasa, sheikh salihu Imam Bauchi

Duk 'yan kannywood 'yan iska ne fasikai ne zindikai shedanu masu yada fasadi a bayan kasa, sheikh salihu Imam Bauchi

Babban shehin malami Sheikh salihu imam Bauchi yayi tumu tumu da yan kannywood a cikin wani faifan bidiyo a wajen majalisin karatunsa.

Malam yayi wannan sakon ne zuwa ga yan kannywood inda a cikin kalaman sa ga abinda malamin ke fadi.

“Yanzu wadannan fasikai mujirumai yan kannywood dukaninsu yan iska ne, kasan wani zai ce a tantance babu wani tantance duk yan iska ne, kaga irin fasadin da sunka kai a garin kano sunka tsunduma al’ummar manzon Allah (s.a.w) , duk yan iska ne idan da baban ka a ciki dan iska ne, kunga yadda sunka hantsula bayin Allah, sunka rikata mutanen da suke da alaƙa da tarbiyya da al’ada mai kyau.

Yanzu yar musulmi kakanta musulmi kakarta musulma amma akan kwadayin da son abin duniya tazo bata jin kunyar kowa , a cikin juri’arsu babu wanda zai cemata tsaya a nan.saboda wani dan iska mawaki wani dan iska darakta ya hantsalar da ita, bata ganin kowa ƙimar Alkur’ani da hadisan manzon Allah (s.a.w) basa ganin darajarsu.

Haka shima wannan yaron an fitar da shi daga cikin layin mutanen manzon Allah baya jin kunyar kowa saboda a wannan al’amari naga wani sheɗanin yaro har malamai yake yiwa gargadi, saboda wani dan wasan kwaikwayon Allah ya matsi bakinsa yazo ya falasa tsiyar da suke ya fassara ya bayyana yace hakane kuma anayin .

Malam ya ƙara da cewa sai wani yazo yana yiwa malamai gargadi, yana cewa muma malamai muna da irinku da zasu cika su ci mutuncin malamai, kar malamai su shiga to yanzu malamin addini zaka baiwa tsoro ae wallahi baka isa ba – inji sheikh salihu.

Malam yayiwa yan kannywood kudin goro tare da wankin babban bargo wanda yayi musu tas wanda wannan karatun mai zafi ne sai da ayi hakuri.

Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button