FEDERAL GOVERNMENT SABON TALLAFI GA MAGIDANTA MILLIYAN 15 A FADIN KASA.

FG N25000 CASH TRANSFER

Labaran Hausa

  • Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin kwashe masu tabin hankali a kan tituna zuwa aisbiti

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin kwashe illahirin masu larurar ƙwaƙwalwa da ke gararamba a kan titunan jihar a birni da ƙauye.

    Fauziyya D Sulaiman, hadima ta musamman ga Gwamnan kan harkokin jin-ƙai ce ta shaida hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na facebook a yau Talata.

    Ta ce gwamnan ya bada umarnin ne bayan koke-koken da al’umma su ka shigar ga gwamman.

    Ta kara da cewa tuni dai aka fara aikin kwashe masu larurar zuwa asibitlcin masu larurar ƙwaƙwalwa domin kulawa da lafiyar su.

    “Bayan koke-koke da aka shigar gurin mai girma Gwabnan Kano H.E Abba Kabir Yusuf akan masu larurar kwakwalwa da ke yawo akan titunan Kano cikin birni da kauye wasunsu ma tsirara suke yawo, wasu ana cutar da rayuwarsu musamman mata, kuma ba su da galihun da zaa dauke su akai su asibiti, mai girma Gwabna ya bayar da umarnin a kwashesu akai su Asibitin masu Larurar kwakwalwa domin kulawa da lafiyarsu.

    “Yau muka fara wannan aikin karkashin hukumar Agajin gaggawa (SEMA) da kuma office dina, SSA Needy and Valnurble,” in ji ta.

  • Nasara ga Azzalumi na karamin lokaci ne kawai kamar dai yadda Allah ya bawa Fir’aauna dama, Sanusi Lamido

    Tsohon sarkin kano Muhammadu Sanusi Lamido Na II a wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumintar zamani an hango shi Yana cewa Idan kana tare da Allah karka ji Tsoron wanda yace shi ba Ruwansa da Allah domin ko da yayi wata Nasara ko galaba ta dan lokaci ne Dan Kadan, kuyi hakuri za ku ga karshen al’amarin yadda zai kare watakila Allah ya bashi dama ne domin ya halaka shi, ku duba fir’auna babu Abinda Baiyi ba kafin zuwan Annabi Musa da bayan zuwansa amma Annabi Musa yace kuyi hakuri Ubangiji zai halaka makiyinku Kuma haka Allah ya yi daga karshe.

    Jama’a da dama na cewa wannan furuci na Muhammadu Sanusi Lamido na da nasaba ne da dambarwar Yanke hukuncin shari’ar jihar Kano.

    Wani labarin : Shari’ar Zaben Gwamnan jihar Kano Kotun daukaka Kara na Shirin sauya ra’ayin jama’a Zuwa ra’ayin Siyasa – Jega.

    Tsohon Shugaban Hukumar Zabe INEC Farfesa Attahiru Jega Yace Kuskuren Kotun Daukaka Kara A kam Zaben Gwamnan Jihar Kano Abin Takai ne Ana Bukatar A Yi Cikakken Bincike.

    Farfesa Jega jiya a lokacin da yake fira da gidan Television na Channel
    ya yi Allah-wadai da hukuncin kotun daukaka kara ta jihar Kano, ya kuma zargi bangaren shari’a da yunkurin sauya ra’ayin jama’a domin ra’ayin Siyasa.

  • A wata al’ada: dole goggon Amarya tayi jima’i da Ango domin ta gwada karfin sa

    Wata Al’adar da wasu mutane ke yi yayin da A ka ɗaura Auren Budurwa a yankin su ta bukatar gwajin budurci daga amarya da kuma karfin iyawa daga ango wanda za a gwada shi da goggon amarya.

    Matan da ke Banyakole a ƙasar Uganda suna da wata Al’ada wacce idan za a miki Aure tilas ne goggon ki ta zama miki babbar ƙawa saboda ƙauna da Soyayya da kuma jagorantar ‘yar uwarta ta hanyar zama aminiya ga ƴar yayarta musamman kan abubuwan da ba za ta iya rabawa da mahaifiyarta ba.

    Domin a wajen ƙabilar Banyakole na Uganda, aikin inna ya wuce yin nasiha kawai har ma da ɗaukar duk wani nauyi da ya gagari Amarya ta yi shi tare da mahaifiyar ta a al’adance.
    Mutanen Banyakole wadanda kuma ake kira da kabilar Ankole mazauna Masarautar Bantu ce wacce ta samo asali tun daga karni na 15. Tana cikin Kudu maso Yammacin Uganda, gabas da Tafkin Edward, masarautar da Sarki Mugabe ke mulki wacce ta shahara da kare haƙƙin aure na musamman.

    Auren Banyakole:

    Aure a cikin wannan al’ada yana da mahimmancin gaske yayin da iyaye ke samun farin ciki da alfahari daga auren ‘ya’yansu. A bisa al’adar Banyakole, idan yarinya ta kai shekara takwas ko tara, aikin inna ne ta gyara ta don rayuwar iyali. Goggon ta za ta koya mata duk wani abu daya kamata ta sani game da matsayinta na mace mafi mahimmanci, a matsayin matar aure.

    Budurci a cikin wannan al’ada ana girmama shi sosai don haka dole ne ‘yan mata su kaurace wa yin jima’i kafin aure. Kuma idan aka gano yarinya ba budurwa ba ce kafin aure, to za ta fuskanci hukuncin kisa ko yanke mata hukunci daga al’umma.

    Bugu da ƙari, mutanen Ankole suna ɗaukar wasu hanyoyi na gyara budurcin Yaran su Don haka lokacin da ‘yan mata suka kai shekaru takwas ko tara, ana bukatar su riƙa yin kitso inda ake ciyar da su gero, naman shanu, da madara. Ana yin wannan galibi don ‘yan mata ko sa sami damar jawo hankalin miji.

    Auren Banyakole ya ƙunshi shagulgula da dama ciki har da lokacin Bayar da kyauta da aka sani da “Kuhingira” inda dangi da abokan amarya ke gabatar mata da kyaututtuka kamar shanu da sauran kayan abinci da za su kai gidanta na aure. Inda bayan kwanaki 10, ana aiwatar da wata al’ada wacce ake kira Okukoza Omunuriro. A nan ne za a sanya Amarya ta ɗora girki ta kunna wutar girkin ta na farko a sabon gidan Mijinta.
    A ranar daurin aure, ana shirya biki a gidan amarya inda mahaifin zai yanka bijimi yayin da a gidan ango kuma akwai wani biki na kara aure.

    Amma da farko, dole ne a yi bikin gargajiya na karshe, bikin da ya kunshi gwaje-gwaje biyu wanda dole ne goggon amarya ta gudanar da shi.

    Tunda budurci shine ma’aunin aure ga matan ƙabilar Banyakole, dole ne kowace amarya a gwada ta da innarta don tabbatar da budurcinta kafin auren. Idan amarya ta wuce gwajin budurci, ana zaton ba ta da ilimin jima’i ko yadda za ta faranta wa sabon mijinta rai ta hanyar jima’i.
    Don haka, gwaji na biyu ya shafi goggon amarya tana gwada ƙarfin jima’in da ango ke da shi ta hanyar yin lalata da shi. A yayin wannan aikin da ake yi a gaban Amarya tana kuma koyon duk dabarun Jima’i da kuma sifofin da aka fi so don ta iya ba wa mijinta gamsuwar da ake buƙata a matsayin ta na Amarya don faranta wa mijinta rai a cikin auren.
    Ya Abin ya ke A Yankin Ku?
    #Dimokuraɗiyya

  • Hotuna: ‘yan watanni kadan bayan shigarsa Musulunci a yanzu ya Rubuta Al-Qur’ani da hannunsa

    Masha Allah labari mai daɗi da majiyarmu ta leadership hausa na ruwaito wani hazaƙin dalibi da Allah ya albarkaci shigowarsa addinin musulunci yayi wata bajinta a duniyar Musulunci.

    ‘Yan watanni bayan ya karbi Addinin Musulunci wani matashi mai sunan Ibrahim ya rubuta Al-kur’ani mai girma da rubutun hannu a garin Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

    Malaminsu Abu Anas Al-baahy ya ce, bayan ya shiga ajinsu na ‘Faslu Imamu Malik Bin Anas’ sai ya tarar da shi da Al-kur’aninsa a gefe yana ta kokarin ganin ya rubuta Al-kur’ani ta hanyar kwafa yana rubuta shi a littafi.

    Malamin na su ya bayyana cewa, hakika ganin haka ya sanya shi tsaya wa cak cike da farin ciki yana kallon ikon Allah.

    Shi dai wannan matashin da sunansa Ibrahim, sunan mahaifinsa Sylvester, watanni biyar baya ko harafin Alifun baya iya furtawa balantana ya rubuta, cikin ikon Allah bayan shigarsa Islamiyyar At-tatbiqul Islamiya, yau ga shi AlQur’anin ma yake kokarin ya rubuce wa duka.

    Ga hotunan a kasa domin ku kalla.

  • Hotuna: Kayataccen gidan da aka kawata shi da zinare mallakar marigayi attajiri Alhaji Mai Deribe a garin Maiduguri

    Marigayi Alhaji Mai Deribe yana daya daga cikin hamshakan masu kudin Afrika da suka mori dukiyarsu kuma har duniya ta dinga sha’awarsu.

    Deribe ya gina wata gagagrumar fada a Maiduguri wacce magina suka kwashe shekaru 10 suna aikinita kafin su kammala.

    Daga cikin manyan mutane a duniya da fadar ta bai wa masauki akwai tsohon shugaban kasar Amurka, Geroge Bush da Olusegun Obasanjo Marigayi Alhaji Mai Deribe babu shakka yana daya daga cikin hamshakan masu kudi a Najeriya a shekarun 1980.

    Ya gina gida wanda aka yi shi da ruwan zinari.

    Mai Deribe yana cikin attajirai guda 12 a duniya da suka mallaki wani jirgin sama mai kirar Gulfstream G550 a shekarar 1971.

    Gidan, wanda ake kira da Gidan Deribe, ya ja hankulan jama’a masu tarin yawa a duniya. Ba abun mamaki bane ganin yadda ya dinga saukar manyan mutane a duniya kamar Yarima Charles da matarsa, marigayiya Gimbiya Diana.

    Wadanda suka taba shiga Gidan Deribe akwai tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Sarki Juan Carlos na kasar Spain da tsohon shugaban kasar Amurka, George Bush. Shugaban kasar mulkin soja na wancan lokacin, Janar Ibrahim Babangida, shi ya jagoranci bude fadar zinarin bayan kammala ginin da aka yi.

    Daga Mustapha Moh’d Gujba.

    Ga hotunan a kasa domin ku kalla.

  • ‘Yan bindiga a jihar Zamfara sun kwashi mutane sama da guda 100 sabida sunki biyan kudin haraji

    Najeriya – ‘Yan ta’addan da suka hana zaman lafiya a sassan jihar Zamfara dake Najeriya sun kwashi mutane sama da 100 a kauyukansu dake yankin Dansadau sakamakon bijirewa biyan harajin naira miliyan N110 da suka dora musu a matsayin kudin kariya.

    Rahotanni daga jihar sun ce ‘yan bindigar da suka kwashi mutanen sun fito ne daga cikin magoya bayan fitaccen ‘dan ta’addan da ake kira Damina, wanda ya addabi mutanen wannan yanki na jihar Zamfara dake iyaka da jihar Kaduna.

    Wani daga cikin mutanen yankin da ya tsallake rijiya da baya, yace tawagar ‘yan bindigar sun mamaye su ne bayan Sallar isha, inda suka musu kawanya, suka kuma tasa keyarsu zuwa cikin daji.

    Daga cikin kauyukan da ‘yan bindigar suka kwashi mutanen da suka hada da mata da yara, akwai Yar Kasuwa da Unguwar Kawo da Kwanar Dutsi da kuma Sabon Garin Mahuta.

    Majiyoyi sun ce Damina ya bai wa mutanen wadannan kauyuka ne mako guda ne domin biyan naira miliyan 110 da ya dora musu, ciki harda naira miliyan 50 da ya dorawa mutanen kauyen Mutunji saboda tseguntawa sojoji yadda suke motsawa a yankin da kuma naira miliyan 30 da ya dorawa mutanen kauyen Kwana da naira miliyan 20 da aka dorawa mutanen Sabon Garin Mahuta, sai kuma naira miliyan 10 na mutanen Unguwar Kawo.

    Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da suka fi fuskantar ta’addancin ‘yan bindiga a Najeriya, wadanda suka mayar da kisa da kuma karbar kudin fansa suka zama ruwan dare.

  • An taba dasamin bomb a ofishi na, cewar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

    Sheikh aiminu Ibrahim daurawa babban kwamandan hisbah ta jihar Kano a cikin wani shiri da rumfar afrika podcast ke gatabarwa take yinda ta tattaunawa da irin gwagwarmayar maya da malam yayi a harka da’awa.

    Sheikh aminu Ibrahim daurawa ya fadi irin tafi nan fada nan da su kayi a rayuwar da’awa shida marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam kano abokin gwagwarmayarsa.

    Sheikh daurawa yace akwai lokacin da har bomb na dasa a ofishin sa saboda kawai a kashe su a hutu.

    Barazanar mutuwar da kisa da ankayimin tafi dari domin naga abokan da’awa ta da anka kashe su ta wannan hanya ashe bada wasa bane, an kai min takarda mutum yafi sau nawa, anyi sakon tarkagwana yafi sau nawa, anje ofishi dina an aje min bomb saboda wata mu’amala da munkayi da waɗanda sunka kawo bomb ɗin ance su dauke.

    Suka ce abin nan da munka kawo bomb ne, amma an mana waya ance mu dauke, ce muna sukayi su yan gudun hijira ne munka basu masauki ashe jikar tasu bomb ce to irin mu’amala da munkayi da su, sunka ce yanzu babu wannan sunka jan ye.- inji sheikh daurawa.

    A cikin tattaunawar nan babban abinda zai baka mamaki shine malam yace ya rubuta wakoki sun fi guda ashirin Wanda yanzu haka ana rera a islamiyoyi, waɗanda ba’a san nina yi sun ba idan na biyo naji ana rerawa yara sai inyi murmushi in wuce.

    Ga cikekkiyar bidiyon a kasa domin ku kalla.

  • ‘Yan bindiga na tursasa wa manoma biyan haraji kafin girbi a arewacin Najeriya

    Manoma a yankin arewa maso yammacin Najeriya sun ce suna cikin halin tsaka mai wuya Sakamakon yadda ‘yan bindiga suke hana garuruwa da dama na yankin yin girbi da kwashe kayan amfanin gona.

    Manoman sun ce ‘yan bindigar kan tilasta masu biyan zakkar amfanin gona da biyan kudi ko kuma idan ba haka ba su kwashe kayan amfanin gonar, ko su kone su kurmus.

    Wani rahoto da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce za a fuskanci a yunwa a arewacin Najeriya sakamakon matsaloli da suka kunshi har da tsaro a yankin.

    Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce ta yi zama da shugabannin mutanen yankin kan yadda za a shawo kan matsalar tsaron.

    Mazauna yankin Birnin Gwari sun ce matsalar ta yi kamari musamman yadda ɓarayi suka addabe su.
    “Ƴan bindigar za su zo ana cikin aikin gona su koma gefen su kasa su tsare bayan an gama tattara amfanin gona an saka a buhu su ce nasu ne.”
    “Sannan za su ce a saya a ba su kuɗin bayan tattara amfanin gonar,” kamar yadda wani mazauni yankin Birnin Gwari ya shaida wa BBC.

    Ya ce manomi ba zai iya kwashe amfanin gonarsa ba har sai ya kammala biyan harajin da ɓarayin suka aza masa.

    “Idan kuma mutum ya gaza biyan kuɗin da suka buƙata, sai dai ya bar amfanin gonar a nan.”
    “Akwai kuma ƴan Ansaru waɗanda ke tilata wa manoma biyan zakka, baya ga ƴan bindiga da ke kwashe amfanin gona”
    “Wannan matsala ta tilasta wa mutane da dama yin gudun hijira.” in ji shi.
    Manoma na biyan kuɗin tara a Katsina

    A jihar Katsina ma akwai ƙauyuka kusan shida da ƴan bindigar suka tilasta wa biyan kuɗin tara, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC.

    “Sun aza wa ko wane gari naira dubu ɗari bakwai da ashirin,” a cewar wani mazauni yankin wanda ya ce ɓarayin sun tilasta masu biyan kuɗi kafin girbe amfanin gonarsu
    Ya ce kowane gari idan ya haɗa za a tafi a kai wa ɓarayin .
    Matsalar hana girbi da kwasar amfanin gona da yan bindiga ke yi a yankin arewacin Najeriya wani ƙarin ƙalubale ne ga batun samar da abinci a daidai lokacin da ƴan ƙasar ke kukan matsalar matsin tallalin arziki.

    Rahoton hukumar samar da abinci ta majalisar ɗinkin duniya ya ce mutum sama da miliyan 16.5 ke fuskantar barazanar yunwa a yankin arewacin Najeriya daga Oktoba zuwa Disamban 2023.
    Sannan matalar za ta fi ƙamari a 2024 inda mutum miliyan 26 za su fuskanci barazanar yunwa a yankin na Najeriya da ta fi arziki a Afirka.

  • Dan keke Napep ya tsinci kudi kimanin naira Milyan 9 ya maidawa mai shi a jihar Yobe

    A yau din nan majiyarmu ta samu wani Kyakykyawan labari wanda tabbas wannan matashi yayi abun bajinta da ya kamata a jinjina masa irin wannan gudun abin duniya da haram na mayar da kudi duk da ana cikin tsananin farata da yunda da tsadar rayuwa.

    Wani ma’aboci mai amfani da kafar sada zumunta Jauro Ahmad ya ruwaito wannan labari a shafinsa na sada zumunta inda wani matashi yayi abin kokari inda yake cewa.

    “Wannan shine Ari Bulama Aji (Ari Luu) Mai Sana’ar Achaba Da Tsohuwar NAPEP Dake Garin Jumbam , Karamar Hukumar Tarmuwa A Jahar Yobe, Wanda Ya Tsinchi Kudi Har Naira Miliyan Tara.

    Ba Tare Da Bata Lokaci Ba Ya Mayar Da Kudin Da Ya Tsinta

    Lamarin Ya Faru Ne Sati Daya Gabata (17/11/2023)

    Allah Ya Kara Mana Irinsa A Chikin Alummah.”

  • Kotu ta raba auren shekara 10 bisa matsawar mahaifin matar na arabu kan za ai wa ‘yarsa kishiya

    Kotun Shari’ar Muslunci da ke zaman ta a hukumar Hisbah ta jihar Kano ta datse igiyar auren wasu ma’aurata bayan sun shafe shekaru 10 tare.

    Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tun da fari ne matar, Amina Muhammad, ta kai ƙarar mijin nata, Aliyu Abdurraham Aliyu, inda take neman a raba auren su saboda bata don a yi mata kishiya.

    Wannan jaridar ta kuma rawaito cewa ana zargin mahaifin matar, wanda Hakimi ne a wata ƙaramar hukuma a Kano, shi ya matsa sai an raba auren bisa hujjar cewa su gidansu na sarauta, ba a yi wa ƴaƴansu kishiya.

    Saidai a zaman Kotun na jiya Litinin, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Sani Tanimu Sani Hausawa ya datse igiyar auren bayan ya karbi rokon lauyan Amina, Barista Ibrahim Umar Musa tunda an kasa samun daidaito a tsakaninsu.

    A hukuncin ‘, Mai sharia Sani Tanimu Sani Hausawa ya nemi wacce tayi Kara data biya kudin Kul’i naira dubu 20 ‘, amma shi wanda a ka yi kara yana da damar daukaka kara zuwa Kotun gaba.

    A zaman Kotun na farko, Lauyan wanda aka yi kara, Umar Yusuf Khalid ya bayyana damuwarsa kan yadda aka kasa samun daidaito, inda ya yi nuni da cewa sabani a zaman aure ba bakon abu bane.

    Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a zaman kotun na baya, alkalin kotun ya umarci mijin da ya yi bikin matar sa, inda lauyan ta ya nemi ya tafi da kaji, kuma hakan aka yi, amma ko da ya je, sai aka ki bashi matar, har sai da ta kai ga kotu ta datse igiyar auren.

    Abin jira a gani shi ne ko mijin, Aliyu zai daukaka kara domin ganin ya karvi ƴaƴansu 4 da suka haifa.

Back to top button