FEDERAL GOVERNMENT SABON TALLAFI GA MAGIDANTA MILLIYAN 15 A FADIN KASA.

FG N25000 CASH TRANSFER

Kannywood

 • Abdul Amart Maikwashewa ya bayyana dalilin sayawa iyalan marigayi Aminu S Bono gida

  Fitaccen maishirya fina finan Hausa Abdul Amat Mai Kwashewa ya sayawa iyalan Marigayi Aminu S. Bono gida na sama da naira miliyan uku.

  Da yake zantawa da Kanawa Radio jim kadan bayan kammala addu’o’i na musamman da kungiyar masu Bada umarni ta shirya a yammacin ranar Litinin a birnin Kano.

  Mai kwashewa yace Aminu S. Bono na daga cikin mutanen da suka taimaka wajan kawo cigaba a kamfaninsa, saboda haka duk abinda yayiwa iyalinsa bai fadi ba.

  A cewar sa, “Aminu S. Bono ya na daga cikin wadanda su ka taimakawa kamfani na na ABNUR Entertainment ya kai matakin da ya ke a yanzu”.

  Ya kuke ganin irin wadannan abubuwan arziki da ‘yan Kannywood din keyiwa iyalan Marigayin.

  A yau da munka zo sadakan bakwai nake ake cewa kamar wannan watan kuɗin hayar gidansa zai karewa sai nace to dan Allah a nemo gida kusa ga iyayensa kuma alhamdullahi anka samu duk da ban shirya hakan ba amma kuma an saye, babban abinda munka tattauna da yan uwana shine ta yadda zamu samarwa da iyalana jari babba da zasu iya cigaba da kasuwanci saboda halin yau da kullum.

  Nagudu tv sun samu tattaunawa da Abdul amart mai kashewa tun daga can wajen sadakan bakwai inda bayyana dalilan sa.

  Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.

 • Duk ‘yan kannywood ‘yan iska ne fasikai ne zindikai shedanu masu yada fasadi a bayan kasa, sheikh salihu Imam Bauchi

  Babban shehin malami Sheikh salihu imam Bauchi yayi tumu tumu da yan kannywood a cikin wani faifan bidiyo a wajen majalisin karatunsa.

  Malam yayi wannan sakon ne zuwa ga yan kannywood inda a cikin kalaman sa ga abinda malamin ke fadi.

  “Yanzu wadannan fasikai mujirumai yan kannywood dukaninsu yan iska ne, kasan wani zai ce a tantance babu wani tantance duk yan iska ne, kaga irin fasadin da sunka kai a garin kano sunka tsunduma al’ummar manzon Allah (s.a.w) , duk yan iska ne idan da baban ka a ciki dan iska ne, kunga yadda sunka hantsula bayin Allah, sunka rikata mutanen da suke da alaƙa da tarbiyya da al’ada mai kyau.

  Yanzu yar musulmi kakanta musulmi kakarta musulma amma akan kwadayin da son abin duniya tazo bata jin kunyar kowa , a cikin juri’arsu babu wanda zai cemata tsaya a nan.saboda wani dan iska mawaki wani dan iska darakta ya hantsalar da ita, bata ganin kowa ƙimar Alkur’ani da hadisan manzon Allah (s.a.w) basa ganin darajarsu.

  Haka shima wannan yaron an fitar da shi daga cikin layin mutanen manzon Allah baya jin kunyar kowa saboda a wannan al’amari naga wani sheɗanin yaro har malamai yake yiwa gargadi, saboda wani dan wasan kwaikwayon Allah ya matsi bakinsa yazo ya falasa tsiyar da suke ya fassara ya bayyana yace hakane kuma anayin .

  Malam ya ƙara da cewa sai wani yazo yana yiwa malamai gargadi, yana cewa muma malamai muna da irinku da zasu cika su ci mutuncin malamai, kar malamai su shiga to yanzu malamin addini zaka baiwa tsoro ae wallahi baka isa ba – inji sheikh salihu.

  Malam yayiwa yan kannywood kudin goro tare da wankin babban bargo wanda yayi musu tas wanda wannan karatun mai zafi ne sai da ayi hakuri.

  Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.

 • Madalla Maikwashewa: Abdul Amart Maikwashewa ya sayawa iyalan Aminu s Bono gida

  A yau din nan Ƙungiyar Daraktoci ta PROFDA na gayyatar dukkan ƴan wannan masana’anta mai albarka ta Kannywood, zuwa taron addu’ar ɗan uwan su marigayi Aminu S. Bono.

  Rana: Litinin 27-11-2023
  Wuri: Social Welfare, Court road
  Lokaci: 3:00 na yamma.

  Allah ya bawa kowa ikon zuwa, a ranan zasu saka dukkan ƴan uwan su da suka riga mu gidan gaskiya acikin Addu’a kamar yadda sunka fitar da sanarwa jiya.

  A wajen ne anka samu labari mai dadi babban mai shiryawa furodusa yayiwa iyalan margayi mai bada umurni darakta Aminu s bono goma ta arziki kamar yadda daya daga cikin yan masana’atar Kannywaood na fitar da labarin a shafinsa na sada zumunta Al-amin chiroma.

  Babban Furodusa, Abdul AMART, Wanda aka Fi sai da Mai Kwashewa, ya saya wa iyalan Marigayi Director Amuni S. Bono Gidan zama.

  Masana’antar Kannywood na ci gaba da yi wa Abdul Amart godiya marar adadi, gami da addu’ar Allah Ta’ala Ya saka masa da mafificin alheri, ameeen.

  A daidai lokacin da ake ci gaba karanta addu’o’in fida’i ga ruhin Malam Aminu Suraj Bono. Allah Ya rahamshe shi, ameeeeen.

 • Na yafewa marigayi Aminu s bono duk kudi da nake binsa,cewar Murja Ibrahim Kunya

  Shahararriyar mai amfani da kafar yanar gizo ta TikTok ‘yar asalin jihar Kano Murja Ibrahim Kunya ta bayyana cewar dukkan kudaden da take bin marigayi Darakta Aminu S Bono ta yafe masa.

  Murja yayin da take mayar da martani a kan kiran da aka yi mata na cewar ta bayyana adadin kudaden da take bin marigayin.

  Ta bayyana cewar har ga Allah ta yafe masa kudaden, kuma bata bukatar a biya ta.

  Murja ta kara da cewar ita kanta idan da za ta ga wani wanda yake bin Aminu bashin kudi idan tana da su za ta biya masa ba tare da da wani bata lokaci ba.

  Daga karshe ta yi masa addu’oin samun rahama inda ta ce tana yi masa fatan Allah ya karbi bakuncinsa ya kuma kyautata makwancinsa.

 • Muhimman abubuwan da aka tattauna tsakin kungiyar hisbah da ‘yan kannywood

  Bayan ce-ce-ku-ce, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sake zama da daraktoci da furdusoshi da jarumai da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood don tsaftace harkar fim da nufin kau da ayyukan badala a jihar.

  A jawabansu daban-daban, Shugaban Kungiyar MOPPAN ta Kasa Dokta Ahmad Sarari da takwaransa na Jihar Kano Ado Ahmad Gidan Dabino da Shugaban Kungiyar Jarumai Alasan Kwalle sun nuna jin dadinsu game da taron inda suka sha alwashin ba wa Hisbah goyon baya tare da alkawarin cewa nan gaba za a samu gyara a harkar fim din.

  Jaridar aminiya hausa na ruwaito.Wannan shi ya kawo karshen ce-ce ku-cen da aka yi ta yi game da ganawar Hukumar da ’yan fim na farko, wanda mafi yawansu suka kaurace wa bisa hujjar cewa Hisbar ba ta bi hanyar da ta dace wajen gayyatar su ba.

  Hukumar ta sake mika musu goron gayyata a karo na biyu wanda suka amsa a karkashin jagorancin dan gidansu wato Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano Abba Almustapha.

  Kwamanda-Janar na Hukumar Hisbah Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa korafe-korafe da suke yawan samu daga Kanawa da sauran sassan Najeriya kan yadda ’yan fim ke nuna abubuwan da suka saba wa addinin Musulunci da al’adun Hausawa a cikin finafinansu ya sa suka ga dacewar zama da masu ruwa da tsaki a harkar fim don lalubo hanyoyin kawo gyara a cikin harkar.

  “Ita Hukumar Hisbah an kafa ta ne don ta saita al’umma a kan koyarwar addinin tare da yi musu katanga daga aikata munanan ayyuka.

  “Muna so a lalubo hanyoyin da za a rage nuna abubuwa da suke na tir tare da ci gaba da nuna abubuwa da za su dabbaka addinin da kyawawan koyarwar al’adun Hausawa a harkar fim,” in ji Daurawa.

  A nasa bangaren, Abba Almustapha ya bayyana cewa tuni ’yan fim din suka amince za su zama masu bin doka.

  Abba Almustapha ya jaddada cewa nan ba da dadewa ba hukumomin biyu za su shirya taron kara wa juna sani da ’yayan Kannywood don ilimintar da su kan abin da ya shafi fim ta fuskar addinin Musulunci inda za a gayyato fitattun malaman Musulunci don tattauna tare da lalubo hanyoyin da za a kai harkar fim din ga tudun mun tsira.

 • Irin mutuwar Darakta Aminu S Bono tana bukatar a binciki gawarsa domin gano sababin mutuwarsa

  Mutuwar fitaccen jarumi mai bada umurni a hausa fim aminu s bono ya sanya wasu yan arewa cewa yakamata a yi bincike mutuwar jarumin ta fuju’a da yayi saboda a wasu dalillai da sunka kawo.

  Zamu fara da ra’ayin Aliyu dahiru aliyu wanda fitaccen ma’aboci da kafar sada zumunta ta facebook inda ya bayyana ra’ayinsa kamar haka.

  “Irin mutuwar Aminu S. Bono tana bukatar a yi mata autopsy a gano me ya kasheshi. Haka kawai ana zaune kalau da mutum a ce cikinsa ya murda kuma wai ya mutu ya saba da al’ada, musamman ga mutumin da aka san ya shiga rigimar addini ko ta siyasa.

  Binciken me ya kashe mamaci yana hana a yi masa addu’a ne? Shirme ne a ce ana bukatar a binciki me ya kashe mutum kai kuma ka ce “kawai addu’a za a yi masa.” Ba za a iya hada biyun ba ne?

  Masu cewa kuma binciken me ya kashe mutum (autopsy) rashin tauhidi ne jahilai ne na gaske. Don ba ka ganin abin da ya kashe mutum sai ka ce binciken abin da ya kasheshin rashin tauhidi ne?

  Yanzu da yanka wani aka yi ka ga jini za ka ce kawai a wuce gurin Allah ne ya kasheshi ne? Ko ba a iya kashe mutum da abin da ba a gani ne? Meye laifin bincike kawai don a magance matsala idan da an sameta don gaba?.

  Daga cikin abin da nake rokon Allah akan mutuwa akwai fatan na mutu da daddare a asibiti mai kyau. Don wasu dogon suma suke da safe a binnesu bayan awa biyu. To sai ka ga a marasa lafiyar turawa wasu sun shekara a dogon suma (coma) kuma sun farfado sun ci gaba da rayuwa. Amma mu a nan ka taba ganin wanda aka ce ya yi 24-hours a sume ba a binneshi ba? Sai dai idan a asibiti ne, su ma wasu idan ba a cika musu kudinsu sun saki mutum an binneshi da ransa ba.

  Cewa aka yi idan mutum ya mutu to a gaggauta yi masa jana’iza. Ba wai cewa aka yi ku yi gaggawar binne mutumin da ba ku tabbatar ya mutu ba. Ku dinga kai gawarwaki asibiti domin tabbatar da mutuwarsu.”

  Ita ma hajiya Rahma abdulmajid tana daga cikin masu amfani da kafar sada zumunta inda itama ta bayyana ra’ayin ta da cewa yana da kyau ayi bincike irin wannan mutuwar duba da irin hujjojin da ta kawo.

  “MUTUWAR AMINU BONO…

  Wannan ita ce mutuwar Fuj’ah ta biyu da wani Director yayi a Kannywood. Shin lokaci bai yi ba ke nan da za a rika rungumar binciken zamani irin Autopsy don gane musababban irin wannan farat daya?
  A fahimta fa, binciken musababbin mutuwa ba ja da kaddara ba ne, kawai sanin musababbi ne, wanda zai iya zama sanadiyyar ceton wasu ko gano masu hannu a wani laifin.

  ALLAH YA JIKAN MALAM AMINU”

 • Zan biya duk bashin da ake bin Aminu S Bono, cewar Aisha Humaira

  Fitacciyar jaruma nan makusanciya ga mawakin siyasar nijeriya Aisha Humaira ta fitar da sanarwa zata biya bashin duk wanda yake bin margayi darakta aminu s bono bashi.

  Aisha Humaira ta fitar da wannan sanarwa ta faifan bidiyo tun jiya bayan sanar da mutuwarsa inda ta fadi yadda za’a tuntubeta domin kayi bayanin kowa kake binsa da yadda za’a turamaka kuɗinka.

  “Tabbas mutumin kirkiri ne Aminu s bono aminina yana sona sosai domin yakan bani shawara akan duk abinda zai shafeni na aiki ko kama mancin haka zai fadi shawara sosai.

  Aninu s bono na dade da shi tsawon rayuwa amma ko sa’insa bata tabamu da shi ba, to irin soyayya da kauna da ya nunamin naga babu abinda ya ragemin sai nayi masa addu’a da kuma fatan yiwa mutane rokon dan Allah duk wanda yayiwa ba daidai ba ya yafi masa.

  Game da bashi kuma domin insha Allah duk wanda yake biyarsa bashi in bai fi karfina ba zan biya masa, idan kuma ya fi karfina zan nema masa taimako.

  Zan saka numbobin mutane biyu da suke makusanta aminu s bono domin duk wanda yake binsa bashi sai ya kira yayi bayyani.

  +234 806 084 0990 Hamza Dogo

  0803 888 1014 G Boy”

 • Irin Mutuwar Aminu S Bono Tana Bukatar A Binciki Gawarsa Domin Gano Sababin Mutuwarsa, Cewar Aliyu Dahiru Aliyu

  Irin mutuwar Aminu S. Bono tana bukatar a yi mata autopsy a gano me ya kasheshi. Haka kawai ana zaune kalau da mutum a ce cikinsa ya murda kuma wai ya mutu ya saba da al’ada, musamman ga mutumin da aka san ya shiga rigimar addini ko ta siyasa.

  Binciken me ya kashe mamaci yana hana a yi masa addu’a ne? Shirme ne a ce ana bukatar a binciki me ya kashe mutum kai kuma ka ce “kawai addu’a za a yi masa.” Ba za a iya hada biyun ba ne?

  Masu cewa kuma binciken me ya kashe mutum (autopsy) rashin tauhidi ne jahilai ne na gaske. Don ba ka ganin abin da ya kashe mutum sai ka ce binciken abin da ya kasheshin rashin tauhidi ne?

  Yanzu da yanka wani aka yi ka ga jini za ka ce kawai a wuce gurin Allah ne ya kasheshi ne? Ko ba a iya kashe mutum da abin da ba a gani ne? Meye laifin bincike kawai don a magance matsala idan da an sameta don gaba?

 • Hotunan jana’izar fitaccen daraktan masana’antar kannywood Aminu S Bono

  Hotunan jana’izar fitaccen daraktan Kannywood, Aminu S. Bono wanda ya rasu da yammacin jiya Litinin.

  Manyan ‘yan masana’antar ta Kannywood da dama ne suka halarci jana’izar a unguwar Ɗandago da ke birnin Kano.

  Ga hotunan nan kasa.

 • Abin da yasa muka dakatar da jaruma khadija mai munfashi, cewar Abba El-mustapha

  Shugaban hukumar tace fina finai da dabi’u a jihar Kano abba elmustapha yayi karin haske akan dakatar da wata jaruma mai suna khadia mai munfashi na tsawon shekaru biyu a Masana’atar Kannywood.

  Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Kano Malam Abba Almustapha ya yiwa Freedom Radio karin bayani kan dalilansu na dakatar da Jaruma Khadija Mai Numfashi daga Kannywood har tsahon shekaru biyu.

  “Assalamu alaikum wato bidiyo ne ya yadu/bazu yadda suke zuwa suna raye raye na rashin kamun kai , na tozarci wanda babu daɗi kuma kowa yasan irin yadda korafe korafen da muke karba a koda yaushe mun kirata domin ta kare kanta, ya akayi tabari tana yar masana’atar kannywood da ake bata tarbiyya kada ta yarda tana irin wadannan abubuwan da zasu iya jawo cece kuce.

  Wanda zai iya zamo illa ga al’ummar jihar kano, ko kuma makalla tanmu na shirye shiryen mu kada mu saka kanmu irin wadannan raye raye amma ta saki wannan bidiyo na gidan rawa, mun kirata domin muji daga gareta abun ya faskara.

  Babban laifin da zakayiwa hukumar mu ,mu kiraka ka kasa gayyatarmu- inji abba almustapha.

  Mun kirawo ta tace bata gari yaushe zaki dawo garin , ta dawo garin mun san tana garin tazo koda mu samu sasauci ne muji daga gareta koda mu tsawatar mata taki ta bari.

  Saboda haka wannan shine hukuncin da muka dauka a yanzu bara mugani zuwa nan gaba”- inji abba almustapha.

Back to top button