Labaran Hausa

Bayan fitar da kundin hukuncin shari’ar zaben gwamnan jihar Kano

Bayan fitar da kundin hukuncin shari’ar zaben gwamnan jihar Kano da kotun daukaka kara dake Abuja tayi, bayanan da kundin ya kunsa ya haifar da rudani a jahar da kuma kasa baki daya.

A cikin kundin anga wani shafi dake nuni da cewar kotun daukaka kara tayi watsi da hukuncin kotun korafe-korafen zabe ta jahar Kano tare da bayyana Gwamna Abba Kabir Yusif a matsayin wanda yayi nasara.

Related Articles

A gefe guda, Kwamishinan Shari’a na jihar Kano Haruna Isa-Dederi, yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa, ya ce kundin shari’ar ya tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir na Jam’iyyar NNPP sabanin abin da aka sani cewa ta kwace kujerar ta sa.

Saidai har yanzu kotun daukaka kara batace komai game da wannan batu ba, ita jam’iyyar APC tayi gum da bakin ta.

Menene fahimtarku akan wannan al’amari?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button