Ba Zan Taba Fitowa a Fim da Ya Ci Mutuncin Al’adar Hausawa Ba’, Aisha Najamu

Jarumar masana’antar fina-finan Kannywood, Aisha Najamu wacce aka fi sani da Aisha Izzar So, ta bayyana cewa ba za ta taɓa fitowa a fim ɗin da zai taɓa ƙimar al’adar Hausawa ba.
Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa ta musamman da ta yi da jaridar Daily Trust.
Aisha Najamu wacce haifaffiyar jihar Jigawa ce ta bayyana cewa da farko iyayenta, ba su so ta shiga harkar fim saboda maganganun da ake yaɗa wa a kan masana’antar.
Ta bayyana cewa daga baya ta samu ta shawo kansu, kuma har yanzu ba ta yi abin da zai sanya su yi dana sanin barin ta shiga harkar fim.
Aisha Najamu ta magantu kan fitowa a fim
Da aka tambaye ta ko tana zaɓar fina-finai kafin ta yarda ta fito a cikinsu, sai ta kada baki ta ce:
“Ba batun yin zaɓe ba ne, amma batun yin taka tsantsan. Ku tuna fa muna yin fina-finan Hausa kuma muna da al’adu da ɗabi’u da ƙa’idoji na addini da za mu kare.”
“A matsayina na ƴar arewa kuma uwa, ni ma ina da sunana don kiyayewa da kariya, saboda haka, ba zan iya yarda da kowace rawa ba tare da bin rubutun ba.
A matsayi na, na ƴar Arewa kuma uwa, ina da mutunci na da ƙima ta da zan kare, saboda haka ba zai yiwu na yarda na taka kowace rawa ba, ba tare da na duba abin da labarin ya ƙunsa ba.”
“Muna rayuwa ne a cikin al’ummar da yanzu ta ke karɓar sababbin abubuwa saboda haka ba za mu yi kasadar zubar da ƙimar ɗabi’un mu ba.”
“Kamar yadda na faɗa a baya muna da ɗabi’u da zamu tallata tare da kare su, saboda haka dole sai na duba labarin domin tabbatar da cewa ina yin abin da ya dace. Ba zan taɓa fitowa a fim ɗin da ya ci mutuncin ɗabi’u da al’adun Hausawa ba.”