An samu saɓani tsakanin kamfanonin manyan Attajiran Nigeria guda biyu

Kamfanin BUA ya fitar da dogon jawabi a ranar Juma’ar nan, a matsayin martani ga zargin da kamfanin Dangote Group ya jefe sa da shi.
Kamfanin na BUA ya dauko tarihi tun daga 1991 lokacin da aka yi wahalar sukari, amma sai aka yi sa’a Abdul Samad Rabiu ya na da sukari a ƙasa, sai Aliko Dangote ya nemi a saida masa sukarin, sai a karshe lamarin ya kare a kotu, kamfanin ya ce haka Rabiu ya jajirce na watanni uku.
Har ila yau, kamfanin ya ce ya taba karban aron fili daga Usman Dantata domin ya kafa kamfanin siminti, amma Dangote ya jawo aka karbe filin, wanda a dalilin wannan abin da ya faru a gwamnatin Olusegun Olusegun Obasanjo, BUA ya yi asarar filin da ya karbi aro daga hannun kawun na Dangote, sai bayan shekara Rabiu ya iya komawa harkar sukari, yanzu kamfaninsa ya zarce kowa a yammacin Afrika, a cewar wasikar.
Wasikar ta ce haka kamfanin ya yi ta fama bayan samun lasisin kafa kamfanin siminti, BUA ya ce sam kalubalen nan ba su iya taka masu burki ba.
Amma a wani rahoto da Daily Nigerian ta fitar, an ji kamfanin Dangote ya karyata zargin badakalar kudin waje, ya ja kunnen masu yin sharri.